1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Jam'iyar adawa ta yi ikirarin lashe zabe

Zainab Mohammed Abubakar
December 9, 2016

Duk da cewar hukumar zabe mai zaman kanta ba ta gabatar da sakamakon ba, jam'iyyar adawar ta NPP ta ce sakamakon da ke fito daga mazabu na nuna irin gagarumin nasara da ta samu.

Ghana oppositioneller Kandidat Nana Akufo-Addo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Ghana Nana Akufo-Addo , ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a wannan Larabar.

 

Ya ce "Da sakamakon da aka samu kawo yanzu, mun lashe karin 49 daga cikin yawan kujerun majalisa. Kuma muna da yakinin cewar zaben shugaban kasa ma mun lashe. Sai dai zamu yi dakon sanarwar hukumar zabe"

 

Ghana dai na zama kyakkyawar misalin demokaradiyya a nahiyar Afirka, wadda zabenta ke gudana kusan cikin lumana. Karo biyu tun daga shekarata 2000, al'ummar kasar ke kayar da shugaban da ke kan kujerar mulki.

 

Akwai tafiyar hawainiya a kidayar kuri'un da aka kada, sai dai sakamakon da ke fitowa daga kasar na nuni da cewar, jam'iyyar adawa ta NPP ce ke gaba kana NDC ta shugaba mai ci John Mahama Dramani ke biye da ita.