1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ghana ta bukaci hadin kai don neman diyyar mulkin mallaka

Abdullahi Tanko Bala
November 14, 2023

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga shugabanin Afirka su hada kai wajen neman a biya diyya kan jigilar bayi da aka yi a kan teku a zamanin mulkin mallaka.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Bryan R. Smith/AFP/Getty Images

Wasu kasashen yamma dai a baya bayan nan sun amince cewa an aikata ba daidai ba kan abin da aka yi wa Afirka a lokacin mulkin mallaka kuma tuni gidajen adana tarihi na turai suka fara dawo wa da Afirka kayan tarihi da aka sace.

Karin Bayani: Jamus za ta mayar wa Najeriya da kayan tarihi

Shugaban na Ghana yana yawan magana kan biyan diyya inda ya yi amfani da jawabinsa a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya wajen kira ga kasashen da suka yi wa Afirka mulkin mallaka su amsa girman tasirin abin da suka aikata na mulkin mallaka.