1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ghana ta haramta yi wa mutane zargin maita

October 24, 2023

Majalisar dokokin Ghana ta zartar da kudirin doka kan zargin maita domin kare hakkin al'umma

Zargin maita a kasar Ghana
Zargin maita a kasar GhanaHoto: DW/M. Suuk

Matakin ya biyo bayan kisan wata tsohuwa mai shekaru 90 a garin Kafaba da ke yankin Gonja a gabashin jihar Savana a arewacin Ghana, wacce aka jefe har lahira.

Kungiyoyi masu rajin kare hakkokin bil Adama sun koka a kan jinkirin da shugaban kasar ke yi wajen rattaba hannu kudirin domin zama doka.

Camfe-camfe na tsafi ko zargin tsafi da maita ba sabon abu bane a Ghana. Wadanda a kan zarga da kuma iyalansu kan shiga mawuyacin hali sakamkon wariya ko tswangwama da a kan yi musu.