Ghana ta kaddamar da aikin gina matatar man fetir
August 20, 2024Ghana da ke kasancewa kasa ta biyu da ke da arzikin koko a duniya, ta shiga cikin jerin kasashen da ke karfin arzikin man fetir ne a 2020. Alkaluma sun nuna cewa kasar na fitar da gangar mai 132,000 a kullum tare da makamashin iskar gas mai yawan gaske.
Karin bayani:Ghana ta samu ci gaba ta fuskar arzikin zinare
Matatar man fetir din za ta kasance guda daga cikin ayyukan da za su bunkasa tattalin aryikin kasar, a cewar shugaba Akufo-Addo, a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da shirin a yankin Jomoro da ke kudu masu yammacin kasar.
Karin bayani: Asusun IMF ya sake bai wa Ghana rancen Dala miliyan 360
A wata kididdiga da kungiyar sarrafa albarkatun mai ta nahiyar Afirka ta fitar, ta ce kasashen Afirka ta Yamma na amfani da gangar man fetir 800,000 a kowace rana, wanda kashi 90% bisa 100 daga waje ake shigo da shi.