1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta tsare 'yan ƙasar China

June 6, 2013

'Yan sanda a ƙasar Ghana sun kama wasu baƙi kimanin 166, dake aikin haƙar ma'adinai ta haramtattun hanyoyi.

Ghanaian President John Mahama raises the staff of office after swearing to an oath of office at the Independence Square, Accra in January 7. 2013. Ghanaian President John Dramani Mahama has been sworn-in into office despite a court challenge by the main opposition New Patriotic party, citing alleged voting fraud resulting in the absence of party officials at the swearing-in ceremony attended by nine heads of state. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
John Dramani Mahama, shugaban ƙasar GhanaHoto: Getty Images /AFP

Hukumomi a ƙasar Ghana sun tsare a ƙalla yan ƙasar China 166, waɗanda ke aikin haƙar Gold a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Ofishin jakadancin ƙasar China a Accra da ya fidda sanarwar, ya ruwaito cewa, 'yan sanda sun kama mahaƙa daga ƙasar China kimanin 124 a yankin Ashanti, kana an kama wasu 42 a yankunan tsakiya da yammacin ƙasar. Kuma yanzu mahaƙan ma'adinan da aka kama an turasu birnin Accra inda ake tsare da su a babban birnin ƙasar. Kakakin jami'an shige da ficen ƙasar Ghana, Farancis Paldetti, yace wannan yana daga cikin ayyukan hukumar aiki da cikawa, wanda gwamnatin ƙasar ta kafa domin shawo kan matsalar masu haƙar ma'adinai bisa haramtattun hanyoyi. A watan jiya ne dai shugaba Dramani Mahama, ya kafa wata hukumar aiki da cikawa da za ta magance matsalar haramtattun masu haƙar ma'adinai, waɗanda shugaban yace suna ci gaba da haddasa zaizayar ƙasa, da kuma lalata mahalli.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu