Ghana ta tsaurara matakan yaki da Corona
March 16, 2020. Wadannan sabbin matakan da Shugaba Nana Akufo-Addo ya bayyana yayin jawabin da ya yi wa al'ummar kasar Ghana a ranar Lahadi da maraice sun shafi wasannin motsa jiki ko ayyukan addini a majami'u da masallatai na tsawon makwanni hudu. Akalla mutane shida ne suka kamu da kwayar cutar Corona, lamarin da ya sa fadar mulki ta Accra ta dauki tsauraran matakan yaki da cutar.
Kasar ta Ghana ta kuma sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta rufe kan iyakokinta ga mutanen da ke shigowa daga kasashen da cutar Corona ta fi kamari, inda haramci zai shafi kasashen da aka samu akalla mutane 200 da suka kamu da Corona cikin kwanaki 14 na baya-bayannan.
Dama dai Kasashe da dama na yankin kudu da hamadar Sahara, wadanda suka hada da Afirka ta Kudu da Kenya da Yuganda sun dauki matakan rufe iyakokinsu saboda yaduwa da annobar ke yi a kasashen Afirka, inda na baya-bayannan ta kasance Laberiya..