1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta yi kunnen doki da Najeriya a share fagen shiga CHAN

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Mouhamadou Awal Balarabe
December 23, 2024

An shiga zagayen karshe na neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na masu bugawa a gida, inda Najeriya da Ghana suka tashi babu wanda ya yi wani. Sannan ana dambarwar daukar sabon mai horas da 'yan Super Eagles.

Magoya bayan Ghana sun saba alfahari da babbar kungiyar kwallon kafarsu
Magoya bayan Ghana sun saba alfahari da babbar kungiyar kwallon kafarsuHoto: Gabriel Ahiabor/Shengolpixs/imago images

A karshen mako ne aka gudanar da wasannin zagayen farko na share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka masu wasa a gida wato CHAN 2024. Guinea Conakry ta lallasa Guinea-Bissau da ci 4-1, yayin da Lesotho ta baras da damarta a gaban Angola da ci 0-2. Ita kuwa Zambiya ta bi Mozambik har gida kuma ta doke ta da ci 3- 0, yayin da Eswatini ta bidi kashinta a hanun Madagaskar da ci 0-2. A nasu bangaren Chadi da DR Kwango sun tashi 1-1, amma Kamaru ta lallasa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ci daya mai ban haushi.

Sai dai babu yabo babu fallasa a wasan da Najeriya ta yi da Ghana inda aka tashi 1-1, yayin da Sudan ta Kudu ta doke Ruwanda da 3-2. Ita ma Sudan ta yi nasarar doka Ethiopiya da ci 2-0, yayin da Côte d'Ivoire ta yi wa Burkina Faso cin kaca 2-0. Sai dai Laberiya da Senegal sun tashi 1-1, inda aka samu irin wannan sakamako a karawa da aka yi tsakanin Togo da Nijar. A nata bangaren Moritaniya ta samu nasara a kan Mali da 1-0.

Kasashen na Afirka za su ci gaba da gudanar da wasanninsu har 28 ga watan Disemban 2024 domin tantance ilahirin kasashen da za a dama da su a gasar kwallon Afirka ta 'yan wasa da ke buagawa a gida.

Bayern Munich na ci gaba da jan zarenta a Bundesliga

Thomas Mueller da Leroy Sane sun yi murnar samun nasara a kan Leipzig da ci 5-1Hoto: Ulrich Gamel/kolbert-press/IMAGO

Kungiyoyin kwallon kafa da ake fafatawa da su a Bundesliga sun gudanar da wasannin mako na 15 a kakar-wasa ta 2024 zuwa 2025, inda Eintracht Frankfurt da ke wasa a gida ta yi rashin sa'a saboda Mainz ta doke da ci 3-1. Sai dai Bayer Leverkusen da ke rike da kambin zakara ta yi wa Freiburg dukan kawo wuka 5-1. Haka ita ma Yaya-karama Borussia Dortmund ta bi Wolfsburg har gida kuma ta doke ta ci 3-1. Ita Bochum ta yi abin kai a wannan karon saboda ta mamaye Heidenheim da ci 2-0.

Amma har yanzu Bayern Munich ce ke ci gaba da jan zarenta a samen teburin Bundesliga da maki 36 yayin da Bayer Leverkusen ke biya mata baya da maki 32. Ita kuwa Frankfurt ta yi a matsayi na uku da maki 27, yayin da Bochum ke ci gaba da zama 'yar baya ga dangi da maki shida kacal.

Liverpool na zawarcin Joao Pedro na Brazil

Liverpool na son samun karin kwararrun 'yan wasa ciki har da Joao Pedro na BrazilHoto: David Ramos/Getty Images

Yayin da ya rage kwanaki kalilan a bude kasuwar cinikayyar 'yan wasa a nahiyar Turai, Liverpool ta fara yunkurin sayen dan wasan Brighton kuma 'dan aksar Brazil Joao Pedro. Ita kuwa Paris St-Germain ta Faransa na shirin biyan yuro miliyan 100, kwatankwacin fam miliyan 83 ga Newcastle United don sayen dan wasan gaba na Sweden Alexander Isak. Haka zalika PSG na da muradin biyan fam miliyan 48 ga Athletic Bilbao ta Spain da nufin sayen matashin dan wasan Spain Nico Williams, wanda Manchester United da Barcelona ke hankoron cinikinsa.

A gefe guda kuma Barcelona ta yanke kauna ga dan wasanta na tsakiya dan kasar Holland Frenkie de Jong, wanda alamu ke nuna cewa yana kan hanyarsa ta barin kungiyar. Ita ko Real Madrid na fatan daukar matashin dan wasan Spain Rafa Marin daga Napoli ta Italiya.

Kiki-kaka wajen daukar mai horas da Super Eagles daga Turai

Daga cikin manyan dalilan da ke hana masu horaswa daga Turai karbar jagorancin Super Eagles ta Najeriya shi ne rashin tabbacin samun albashi. Hatta na baya-bayan nan ma Jose Peseiro sai da kotun sauraron kararrakin wasanni ta shiga tsakani, kafin biyan shi kudin watanni 11 da yake bin NFF bashi. A yanzu dai, wani banki da ba a bayyana sunansa ba tare da wani kamfani, sun bayyana cewa za su dauki nauyin biyan albashin duk wani mai horaswar da NFF ta cimma yarjejeniya da shi daga Turai.

Oleksandr Usyk na Ukraine ne sabon sarkin damben MMA

Oleksandr Usyk ya samu nasara a kan Tyson Fury a damben ajin masu nauyi na MMAHoto: Andrew Couldridge/Action Images/Reuters

A fagen dambe, shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya jinjina wa zakaran damben duniya ajin masu nauyi Oleksandr Usyk, bayan da ya lallasa tsohon zakaran duniya Tyson Fury a birnin Riyadh na kasar Saudi Arabiya, yana mai cewar nasara ce babbar abar da suke bukata a wannan lokaci da suke fama da mamaya daga Rasha, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X. Mr Zelenskyy ya kara da cewa 'yan Ukraine ba za su taba karaya ba gwagwarmayar da suke fafatawa, ko a filin yaki ko kuma a filin wasa. Ko a cikin watan Mayun da ya gabata, sai da Oleksandr Usyk ya casa Tyson Fury, kuma shi ne tilo da ya taba doke Fury a rayuwarsa.

Purcell ba zai halarci muhimmiyar gasar tennis a Janairu ba

Hukumar kula da 'da'a ta kwallon Tennis ta duniya ITIA ta zartar da hukuncin dakatar da dan wasan kasar Ostareliya Max Purcell, bayan da ya yi ikirarin karya ka'idojin wasan daban-daban, lamarin da zai haramta masa halartar gasar Australian Open a cikin watan Janairu mai kamawa, sannan za ITIA za ta ci gaba da binciken laifin don tabbatar da hukunci a kai. A baya dai hukumar ta hukunta Jannick Sinner da kuma lamba biyu ta duniya bangaren mata Iga Swiatek a cikin watan Agustan da ya gabata, bayan ta'ammali da mwayoyi masu kara kuzari da aka haramta amfani da su.