Ghana za ta kwaso daruruwan 'ya'yanta daga Afirka ta Kudu
May 13, 2026
Ghana ta sanar da shirin kwaso ‘yan kasarta su 300 daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren kyama da ake kai wa baki daga wasu kasashen Afirka.
Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ce mutane da dama sun nemi taimakon gwamnati domin komawa gida, yayin da gwamnatin kasar ta sha alwashin kare lafiyar ‘yan kasarta a gida da waje.
Hare-haren na kyamar baki a Afirka ta Kudu, sun fusata shugabanni da hukumomi a kasashen nahiyar Afirka da dama.
Duk da cewa hukumomin Afirka ta Kudu sun yi Allah wadai da hare-haren, sun nuna matsalar shige-da-fice ba bisa ka'ida ba da zama cikin dalilan da ke haddasa tashin hankalin.
Kasashe irin su Kenya da Malawi da Lesotho gami da Zimbabwe, sun gargadi ‘yan kasarsu da su yi taka-tsantsan, yayin da Najeriya ta ce akalla ‘yan kasarta 130 su ne suka yi rajistar komawa gida daga Afirka ta Kudun.