1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GHF ta karyata zarginta da batun bacewar mutane a Gaza

August 28, 2025

Kungiyar agajin jinkai a Gaza wato GHF, ta musanta zargin da ake yi mata na cewar ta tilasta bacewar fararen hula da ke neman abinci a Zirin.

Hoto: Stringer/REUTERS

Kungiyar wacce Isra’ila da Amurka ke goyon baya, ita ce ke kula da wuraren raba tallafin jinkai a Gaza.

Masana kare hakkin bil Adama na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sun samu rahotannin cewa mutane da dama, ciki har da wani yaro, sun bace bayan sun ziyarci wasu wuraren rarraba tallafi na kungiyar a Rafah da ke a kudancin Gazar.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta riga ta ayyana yunwa a matsayin wani bangare na wannan yanki na yankin Falasdinu.

Shirin samar da abinci na duniya, ya yi kiran da a sake farfaɗo da cibiyoyin rarraba abinci a fadin Gaza, domin a yanzu kayan abincin da ake shigarwa ta ƙasa ana rarraba su ne kawai a wurare kalilan.