1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghouta:Mutane dubu 105 sun fice daga garin

Abdourahamane Hassane
March 24, 2018

Sama da mutane dubu 1600 suka mutu a gabashin Ghouta kana wasu dubu 105 suka fice daga yankin.

Syrien Qalat al Madiq Geflüchtete aus Ost-Ghouta
Hoto: Getty Images/O. Haj Kadour

Kungiyoyin kare hakin bil Adama da ke saka ido a yakin Siriya sun ce a yanzu gwamnatin Siriyar, ita ce ke da iko da kusan kashi 90 cikin dari na yankunan da 'yan tawayyen kasar suka mamaye bayan kusan wata guda da aka kwashe ana tabkla yaki. Masu aiko da rahotannin sun ce 'yan tawayen wadanda da farko suka ja dagga sun ware daga gabashin Ghouta.