1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Yennenga: Kakar al'ummar Mossi na Burkina Faso

December 10, 2020

Gimbiya Yennenga ta kasance jaruma a fagen yaki kuma kwararriya wajen hawa doki. Ta bar tarihi mai dorewa a Burkina Faso.

African Roots | Yennenga

Yaushe aka haifi Gimbiya Yennenga ?

Masana tarihi basu cimma daidaito ba a game da hakikanin ranar da aka haifi Gimbiya Yennenga, sai dai da dama sun yi imani da cewa an haife ta ne a tsakanin karni na 11 zuwa karni na 15. Ita ce 'yar gaban goshi ta sarki Naba Nedega. Ya yi mulkin masarautar Dagomba wadda a yanzu ta ke cikin kasar Ghana

Mene ne musamman game da Gimbiya Yennenga?

A tarihi ba baka, Gimbiyar ta fi son dokin fiye da sauran dabbobi tun tana yarinya. Bayan shafe tsawon lokaci sau da dama tana yunkuri, Yennega ta sami shawo kan mahaifinta ya kyaleta ta hau doki. Wannan wata dama ce da aka kebe wa maza kawai a masarautar. Gimbiyar ta nuna cewa ba ma kawai tana da hazaka wajen hawa doki bane kadai, jaruma ce a fagen yaki.

Ta haifi danta ne sakamakon soyayya da ta kullu tsakaninta da wani maharbi a daji.

Sun rada wa dan suna Ouedraogo (stallion) domin karrama wannan doki da ya yi sanadiyyar haduwarsu. Kabilar Ouedraogo sune kakannin al'ummar Mossi, kabila mafi girma a Burkina Faso.

Sarkakiya a game da labarinta

Yanayin da Yennenga ta bace a daji ya kasance tamkar al'mara - an rika bada labarai masu karo da juna. Labari mafi shahara shi ne cewa Gimbiyar ta gudu - ta bar kauyensu domin guje wa mahaifinta wanda ya kin yarda 'yar da yake so ta yi aure.

A game da asalin masoyinta kuwa, wasu majiyoyi sun ce mahaibi ne daga kasar Mali. Wannan bayani shine dalilin da ya sa al'ummar Mossi suke da tushe daga Mali.

Wane tarihi ta bari a baya?

A cikin mawaka yan Burkina wadanda suka yi mubaya'a ga Gimbiyar har da Yili Nooma. A gare ta, Yennenga mace ce jajirtacciya kuma wace ba ta da tsoro. jarumar yaki wadda a cikin mata ake so a yi koyi da ita. Sanya sunan Gimbiyar a faifan wakarta ta farko, wata hanya ce ta nuna cewa a yau sune Yennenga a wannan zamani."

An cigaba da raya tarihin Yennenga ta hanyar "Dokin zinare na Yennenga" wanda ake bayarwa ga zakarun da suka lashe gasar fina finai ta FESPACO da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu. A yanzu haka ma ana gina wani sabon birni da aka sanya wa suna Yennenga da kuma ASFA Yennenga kungiyar kwallon kafa ajin farko na gasar Lig ta kasa. Haka ma sunan stallion da aka rada wa kungiyar kwallon kafa ta kasa a Burkina Faso, karramawa ce aka yi ga dokin da Gimbiyar ta fi kauna.

Masanin tarihi Farfesa Doulaye Konaté da Dr Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo sune suka bada shawarwari ta fuskar kimiyya a wannan kasida. Tushen Afirka na samun tallafi daga gidauniyar Gerda Henkel.