Gina gidaje 100,000. bayan girgizar ƙasa a Japan
April 22, 2011Firaministan ƙasar Japan Naoto Kan ya sanar da ƙudurin gwamnatin sa na gina gidajen wucin gadi dubu 100 domin tsugunar da mutanen da matsalar girgizar ƙasa da kuma ambaliyar ruwa ta tsunami ta shafa a watan jiya. Firaministan ya shaidawa manema labarai cewar nan - da ƙarshen watan Mayun dake tafe ne gwamnatin ke fatan kammala gidaje dubu 30 daga cikin adadin dubu 100n.
A yanzun nan da ake batu dai fiye da mutane dubu 100 ne ke samun mafaka a wuraren da gwamnati ta keɓe cikin makarantu da kuma cibiyoyin al'umma, yayin da wasu kuma ke zaune ko dai da 'yan uwansu su ko kuma wurare na wucin gadi.
Tunda farko dai gwamnatin Japan ɗin ta amince da wani ƙaramin kasafin kudin daya kai dalar Amirka miliyan dubu 50 domin taimaka mata ƙoƙarin sake samar da matsugunai ga Japanawan da ke cikin mawuyacin hali sakamakon girgizar ƙasa da matsalar ambaliyar ruwan da aka kwatanta da cewar na daga cikin mafi muni a tarihin bani adamu na baya - bayan nan
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman