Ghana: Za a kashe dala miliyan 200 a gina majalisa
July 4, 2019Talla
Kungiyoyin fararen hula sun kaddamar da kamfe a yanar gizo mai taken #Dropthatchanber wato a jingine batun gina sabuwar majalisa. A cewar kungiyoyin akwai muhimman bukatu da suka sha gaban ginda sabuwar majalisa.
Hukumomi a kasar Ghana na da muhimmanci domin fadada kujerun majalisar daga 275 zuwa kujeru sama da 400. Kasar ta Ghana za ta ranto kudaden aiwatar da aikin ne daga kasar Indiya. Sai dai batun na cigaba da haifar da muhawara tsakanin 'yan kasar da wajen kasar.