Kano: Gina Masallaci ko gina masallata?
October 29, 2025
An dai jima ana samun matsaloli wasu lokutan har da fito na fito a tsakanin mabanbamtan akidu kan mallakar Masalaci, lamarin da a yanzu ya kai zaka ga Masallacin Jumma'a biyu a wuri guda wani lokacin ma katanga daya. Wannan na ci gaba da haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'umma, duk da kasancewar suna addini daya.
Samun Masallatai a waje guda
Ga misali a baya-bayan nan Masallacin Hisbah da ke unguwar Sharada a cikin kwaryar birnin na Kano, an samu cece-kuce kasancewar wani attajiri ya gina Masallaci a jikinsa lamarin. Wannan dai ba shi ne na farko ba, kuma ya zama wani babban lamari da ya dade yana kawo tashin tashina da rikicin addini a Kano.
Yanzu haka dai masana zamantakewar dan Adam kamar Farfesa Sani Lawal Malumfashi na bayyana cewa: "Wajibi ne a samu hadin kai a tsakanin al'umma da galiban malamansu suka koma gasa da juna dan neman tarin mabiya da tasiri." A yanzu dai ana ma hasashen cewa, yawan Masallatai a Kano ya zarta yawan masana'antun da ke jihar.
A ina matsalar take?
To shin meke janyo wannan matsala ne, Shiekh Aminu Khidir limamin Masallacin Jumma'a ne a Kano kuma ya ce: "Ana gina Masallatai ne saboda karfin Musulumci a jihar da kuma ragewa mutane wahalar zuwa Masallaci mai nisa, amma fa akwai takaici kan yadda ake gina wasu Masllatan bisa zafin akida."
Mafita
Koda a hudubobin malamai ma da yawan mutane na kukan yadda yawancin suke kausasa kalamai tare da zagin juna koma a kafirta juna, lamarin da masana ke cewar dole mahukunta su dauki mataki da nufin ragewa yanayin kara yin zafi. Hukumar Shari'a ta jihar Kanon dai ta bayyana cewa, akwai ka'idoji da suka hadar da wajabtawa duk wanda zai gina Masallacin ya zo ya nemi izini a wajensu.