1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Staatsstreich in Guinea Bissau

April 13, 2012

Makonni biyu da rabi gabannin zagaye na biyun zaɓen shugaban ƙasar da ke yankin yammacin Afrika, sojoji sun ƙwace madafan ikon babban birnin ƙasar da ke Bissau.

epa03180815 (FILE) A file photograph showing soldiers at the D'Amura Military Headquarters in Bissau after a military coup d'etat in Bissau, Guinea-Bissau, 01 April 2010. Media reports on 13 April 2012 state that members of the military have taken control of many areas of the capital of Guinea-Bissau and the Presidential Palace of Carlos Gomes Junior has come under attack. EPA/MOUSSA BALDE *** Local Caption *** 00000402100863 +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Tarihi ya sake maimaita kansa a Guinea Bissau. Inda cikin daren juma'ar ce Sojin suka mamaye gidan radiyon gwamnati tare da kai farmaki a harabar priminista Carlos Gomes Junior, mutumin da ake hasashe zai lashe zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da ake shirin gudanarwa. Kakakin jam'iyyar dake mulki ta PAIGC, ya tabbatar da cewar shugaban gwamnatin yana cikin koshin lafiya. Sai dai uwargidan priminista Salome Gomes tace sojojin da suka bijiren, sun kama maigidanta tare da tafi dashi inda ba'a sani ba. Kazalika shima shugaban ƙasa na wucin gadi Raimundo Pereira sojojin sun yi awon gaba dashi. Fernando Peixeiro ɗan jarida ne a kampanin dillancin labarun Guinea Bissau da ake kira LUSA.

"A hukumance babu bayanai dan gane da inda shugabannin biyu suke. Sai dai rahotannin ƙafofin yaɗa labaru na nuni da cewar shugaban gwamnatin rikon kwarya Raimundo Pereira yana tsare a Amura. Amma babu wanda yasan inda priminista Carlos Gomes Junior yake".

Carlos Gomes JuniorHoto: dapd

Jim kaɗan bayan da gidan Radiyo da Talabijin na gwamnati suka daina aiki a yammacin Alhamis, jama'a sun jiwo karar harbin bindigogi. Ayayinda aka harba makamai masu linzami zuwa fadar shugaban kasa. A yanzu haka sojojin da suka tayar da kayar bayan sun mamaye heaquatar jam'iyyar da ke mulki. haila yau sojojin suna girke a dukkan muhimman wuraren, kana suna ziyartar ofisoshin jakadancin ƙasashe daban-daban dake babban birnin na Bissau, domin tattabatar da cewar 'yan siyasa ba su nemi mafa a wuraren ba.

Ɗan jarida Fernado yace..." Daren ya kasance cikin ruɗani. Domin tun da yamamaci ne sojojin suka mamaye tituna, tare da garkame wasu. Tsakanin karfe 8 zuwa 9 kuwa muka fara jin karar harbin manyan bindigogi da rokoki. An rufe hanyar dake zuwa unguwar da gidajen shugaban kasa da Priminista suke. Sakamakon wannan ruɗani dai mutane da dama sun rasa matsugunnensu, a yayin da wasu ke neman yadda zasu tsere daga yankin".

Hoto: picture-alliance/dpa

Halin da ƙasar ke ciki

Sai dai wayewar garin juma'a lamura sun fara lafawa a birnin na Bissau, duk da cewar babu tabbacin dangane da wanda keda madafan iko. Wannan yunkurin juyin mulki dai ya auku ne makonni biyu da rabi gabannin zaɓen shugaban kasa zagaye na biyu, wanda aka tsayar ranar 29 ga wannan na Afrilu da muke ciki. A watan Maris ne aka gudanar da zagayen farko na zaɓen, inda 'yan takara biyu Carlos Gomes Junior da mai bi masa Kumba Yala, suka gaza samun yawan kuri'u da zai basu nasarar maye kujerar shugaban kasar, Malam Bacai Sanha daya rasa ransa a watan janairu.

Masu sanya idanu na ƙasashen yammacin Afrika dai sun yaba wa zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasar ta Guinea Bissau, wadda suka ce an yi shi cikin adalci.To sai dai kisan gilla da akayi wa tsohon shugaban rundunar tsaro na sojin ƙasar Samba Dialo a daren da aka gudanar da zaben na ranar 18 ga watan Maris, ya sake tabbatar da halin rashin tabbas dangane da zaman lafiya a Guinea Bissau, ƙasar dake da tarihin jerin juyin mulki da kisan mummuke na siyasa. Sojojin ƙasar sun yi iƙirarin karbe madafan iko ne domin haifar da sauyi, a maimakon shirin gwamnati na shigar da Sojojin Angola zuwa cikin ƙasar, wadda ake amfani da ita wajen safarar miyagun kwayoyi daga kudancin Amurka zuwa Turai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal