Birnin Akon: Birnin Zamani a Senegal
May 3, 2022Tuni ganye ya fara bushewa a jeji mai girman hecta 500 da ke wajen kauyen Mbodiene, wanda yake tsawon sa'oi biyu na tuki a mota a Arewa maso Gabashin birnin Dakar fadar gwamnatin kasar ta Senegal. Yankin da za a gina birnin na Akon, na dauke da mutanen da suke rayuwa mai sauki. Makiyaya da ke zama a wurin da aka tanadi gina birnin na Akon, na fatan samun karin lokaci da za su ci gaba da rayuwa a yankin. Shi dai wannan birnin ya kasance wanda aka tsara da masana daga bangarori dabam-dabam. Burin shi ne ya zama birnin mai dauke da otel-otel da kamfanonin fasaha na zamani, gami da manyan makarantu masu inganci.
Kasar ta Senegal dai, na cikin wuraren da Akon ya yi rayuwa lokacin da yake karami. A cewar 'yar majalisar dokoki Marieme Soda Ndiaye mutane suna bukatar gidaje masu sauki ne, a ganinta samar da birnin na da kyau ta fannin karfafa yawon bude ido ne kawai. Sai dai ga Yves Thierry Mensah Sakatare Janar na wata kungiyar matasa ta kasar ta Senegal, wannan birnin na zaman wani abu mai muhimmanci na ci-gaba da ya dace a runguma ba a Senegal kadai ba har ta a sauran kasashen Afirka. A shekara ta 2021 ne dai, Akon ya sanar da zai kashe kimanin kudi dalar Amirka miylan 6,000 wajen gina wannan birni. Sai dai har yanzu ana zaman jira.