Ginin hanyoyin dazai hade turai da yankin gabas ta tsakiya da Afrika
January 31, 2007A jiya ne kungiyar tarayyr turai EU ta gabatar da shirinta na samarda hanyoyin tafiye tafiye mafi sauri guda biyar a turai da wasu yankunan kasashen larabawa da Afrika.
Shirin wanda aka gabatar da a birnin Brussels din kasar Belgium a jiya laraba zai hadar da kasashen turai da yankin arewacin Afrika da yankin gabas ta tsakiya wanda zaici kimanin kudi dala billion 58,wanda kuma zaa kammala shi nan da shekara ta 2020.
Bisa ga manufarta na saukaka harkokin sufuri da gajarta lokutan tafiye tafiye ne akan yankunan kan iyakokin kasashen ne ya sanya Hukumar zartarwa ta tarayyar turai ta gabatar da wannan tsari.
Wannan shiri bugu da kari yana da nufin cimma aiwatar da takardun tafiye tafiye na bai daya , da samarda hanyoyi mafi sauki na darajawa dokokin jamian kwastan kwastan,kana ahannu guda kuma da inganta harkokin sufuri baki daya.
Hanyoyin guda biyar zasu hade kashashen Norway da Rasha ,da tsakiyar Turai da tekun Caspian,kana zai biyo ta Ukraine da yankunan Balkans da na kogin maliya zuwa Turkiyya .
Kazalika Hanyar zata bi cikin yankin gabas ta tsakiya da kasashen dake yammacin turai zuwa kudancin Afrika.
Adangane da hakane hukumar gudanarwa na turan ta bayyana cewa ,zata kaddamar da tattaunawa da kasashen dake makwabtaka ,adangane da hanyoyin da zaa samar ta cikin teku da wadanda motoci zasu bi kana dana jiragen kasa.
Komitionar kula da dangantakar ketare Benita Ferrero-Waldner ta bayyana cewa,samarda ingantattun hanyoyi mafi sauri da kasashen dake makwabtaka da turan bawai zai inganta dangantaka tsakaninsu kadai bane,a hannu guda kuma zai dada inganta dangantakar kasuwanci da harkokin yawon shakatawa.
Kakakin sashin kula da harkokin sufuri na kungiyar ta tarayyar turai Michele Cercone ya sanar dacewa wannan aiki na ginin wadannan hanyoyi zaici kimanin euro billion 45,kwatankwacin dalan Amurka billion 58,wanda kuma zaa gudanar dashi har zuwa shekarata 2020.
Sai dai yayi karin bayani dacewa akasarin kasashen dake wannan kungfiya ne zasu dauki nauyin gudanar da aikin a matakansu.
Bangaren Wannan shirin nada nufin fadada tsarin nan na inganta hanyoyin turai ,ko kuma hanyoyi masu muhimmanci daga kasahen dake da wakilci a tarayyar turai,zuwa kasahen dake makwabtaka dasu.Komissionan kula da harkokin fadada kungiyar ta Eu Olli Rehn ya bayyana cewa,fadada wannan shirin hanyoyin kasashen turan zuwa yankin Balkans da Turkiyya ,zai samar da wata kafa na inganta tattalin azriki a wannan yankin baki daya.