1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizan ƙasa mai ƙarfin gaske a ƙasar China ta kashe mutane 300

April 14, 2010

Wata girgizan ƙasa mai ƙarfin gaske data auku a yanmacin ƙasar China ta kashe mutane 300 tare da raunata wasu 800.

Shugaban China Hu JintaoHoto: AP

Wata girgizan ƙasa mai ƙarfin gaske data auku a yanmacin ƙasar China ta kashe  mutane 300 tare da raunata wasu 800. Kanfanin dillancin labaran Jamus ya ruwaito kafofin yaɗa labaran China suna cewar, girgizan ƙasar mai ƙarfin maki 6.9 a ma'aunin girgizan ƙasa, ta auku ne a Yanmacin ƙasar mai tsaunukan gaske.

Yanzu haka dai masu ceto tare da Sojoji na aiki wurjanjan domin ceto mutanen da gine-gine suka ruguje a kansu. Wata jami'ar gwamnatin ƙasar ta Sin ta shedawa kanfanin dillancin labaran AFP cewar, aƙalla mutane 300 ne kawo yanzu suka rasu kana wasu fiye da dama suka samu raunuka daban-daban.

Rahotannin sun kuma ce kashi 85 cikin ɗari na gidajen jama'ar yankin da girgizar ƙasar ta auku duk sun ruguje. Talabijin ɗin ƙasar ta Sin ya nuna wasu hotunan gidajen da suka ruguje.

Kimanin sojojin ƙasar ta Sin 700 ne dai akace suna aiki tare da sauran jami'an kiwon lafiya da taimakon gaggawa domin tallafawa al'umar da bala'in ya aukawa. Akwai dai kimanin mutane dubu 80 a wannan gari na Yushu dake yanmacin Chinan.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita:Umaru Aliyu