Girgizar ƙasa a ƙasar Burma
November 11, 2012![](https://static.dw.com/image/16326139_800.webp)
Talla
Girgizar ƙasar dai ta yi ta'adi ga gine-gine da kuma jikkata mutane da dama a garin na Mandalay da kuma garin Shwebo da ke kusa.
A halin yanzu dai hukumomin Myanmar ɗin sakamakon girgizar ƙasar ta yi sanadiyyar rasuwar muatne biyu yayin da wasu guda biyar su ka ɓace.
A halin yanzu dai ma'aikatan ceto sun duƙufa wajen gano wanda su ka ɓata da kuma tallafawa wanda lamarin ya rutsa da su musamman ma dai a yankunan karkara.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar