1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iThailand

Girgizar kasa a Myanmar da Thailand

Abdullahi Tanko Bala
March 28, 2025

Girgizar kasa ta yi kaca kaca da cibiyar kasuwancin Bangkok da kuma wani yanki na kasar Myanmar

Thailand Bangkok 2025 | Eingestürzte Gebäude auf Baustelle nach Erdbeben
Girgizar kasa a birnin Bangkok na kasar ThailandHoto: Ann Wang/REUTERS

Girgizar kasa da ta auku a Bangkok babban birnin kasar Thailand ta hallaka akalla mutane uku yayin da wasu gommai kuma suka sami raunuka. Mutane da dama a birnin sun jiwo amon girgizar kasar.

Cibiyar nazarin kimiyyar kasa ta Jamus GFZ ta ce girgizar kasar ta fi karfi a makobciya kasar Myanmar kamar yadda bayanan farko suka nuna.

Ita ma cibiyar nazarin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta kai karfin maki da 7.7 a maunin richter tare da kananan amo da suka biyo baya mai karfin maki 6.4.

An ruwaito samun hasarar rayuka a kasashen biyu Thailand da Myanmar sai dai har yanzu ba a san adadin mutanen da lamarin ya shafa ba.

Firaministan Thailand ya ayyana dokar ta baci a Bangkok yayin da Myanmar ta sanar da dokar ta baci a babban birnin da kuma birni na biyu mafi girma a kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW