1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimamin Iftila'in girgizar kasa a Turkiyya da Siriya

Mahmud Yaya Azare
February 7, 2023

Yawan mutanen da suka rasu a girgizar kasar da ta auku a Turkiyya da Siriya sun haura mutum 6,000 yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma jimami

Wani dattijo a Siriya na kukan rashi kan girgizar kasa a yankinsu
Wani dattijo a Siriya na kukan rashi kan girgizar kasa a yankinsuHoto: Aaref Watad/AFP

Bayan mummunar girgizar da ta auku mai karfin maki 7.8 a ma'aunin richter, a daren litinin, kamar yadda masana yanayin kasa suka yi hasashe, an sake yin wata girgizar da ke da karfin maki 7. 6 lamarin da ya kai ga karuwar wadanda suka rasu a iftila'in zuwa mutum 5,600 kamar yadda ma'aikatan ceto suka sanar. 

"Har yanzu bamu da jimillar alkalaman wadanda suka mutu domin wasu iyalan na yin gaban kansu wajen binne gawarwaki ba tare da fada wa mahukunta ba musamman a arewacin Siriya inda ake da tarin buraguzan gidajen da ba a zakulo wadanda ke karkashinsu ba."

Hoto: DHA

A wasu wuraren na yankin Siriya,sakamakon karancin kayyakin aiki da rashin ma'aikatan agaji, mutane na amfani da hannu wajen kawar da buraguzai don tsamo wadanda ke da sauran numfashi. 

Mahukuntan dai sun ce duk da tsananin sanyi da zubar dusar kankarar da ake yi da kuma wata guguwa mai karfi, sun yi nasarar zakulo mutane dubu 7, 840 da ransu daga buraguzan gine-gine, cikin wadanda aka zakulo har da ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ghana Christian Atsu, wanda gini ya rufta masa a yankin Hayat na Turkiyya.

A yanzu dai, mutane na cikin halin damuwa, inda duk da matsanancin sanyi, mutanen ke ci gaba da kwanciya kan tituna, walau saboda gidajensu sun rugurje ko kuma saboda tsoron sake aukuwar girgizar kasar.

Hoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

"Mun gudo zuwa nan ne don tsoron sake aukuwar girgiza kasa domin har yanzu bamu gamsu da bayanan da mahukunta ke bamu cewa babu alamun sake aukuwarta ba, mun gwammace mu zauna nan kan kankara cikin kishirwa da yunwa da ace  mu rasa rayukanmu."

A na dai ci gaba da sukar mahukunta a yankin da kin daukar matakin kandagarki, musamman bayan da wani masanin yanayin kasa dan kasar Denmark, kwanaki auku kafin girgizar kasar yayi has ashen aukuwarta, wacca ya ce, ita ce irinta mafi muni a yankin cikin shekaru 37.

Tuni dai tawogogin agaji daga manyan kasashen duniya da makwabtan kasashen biyu suka isa yankunan da ifttila'in ya faru don ayyukan ceto da agazawa wadanda suka jikkata. A yanzu haka dai an samar da matsugunan wucin gadi ga miliyoyin mutane da wannan iftila’i ya shafa akan iyakokin kasashen biyu.