1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Girgizar kasa kasar Philippines ta hallaka mutane biyu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 4, 2023

Girgizar kasar ta yi tafiyar Kilomita 72 a yankin Hinatuan na tsibirin Mindanao, in da ta fara nuna alamar tayar da igiyar ruwan Tsunami.

Hoto: AFP/Getty Images

Girgizar kasa da ta faru daga tsakar daren jiya Lahadi zuwa asubahin yau Litinin a Kudancin kasar Philippines, ta hallaka mutane biyu tare da raunata wasu da dama, kamar yadda hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka ta sanar.

Karin bayani:China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa

Girgizar kasar ta yi tafiyar Kilomita 72 a yankin Hinatuan na tsibirin Mindanao, kuma ta fara ne tun ranar Asabar zuwa jiya Lahadi har zuwa yau Litinin, in da ta fara nuna alamar tayar da igiyar ruwan Tsunami.

Karin bayani:Biden zai gana da shugaban Philippines

Gine-gine da rufin gidaje sun rushe, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta sanar.