Girgizar kasa mai karfi ta afku a yankin Himalaya na Tibet
January 7, 2025Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta afku a yankin Himalaya na Tibet da ke kudu maso yammacin kasar Sin, inda ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 97 tare da haddasa rugujewar gine-gine da dama. Wannan iftila'in mai karfin awo 6.8 zuwa 7.1 a ma'aunin Richter ya fi shafar garin Dingri inda ake da cunkoson jama'a a kusa da kan iyakar Sin da Nepal .
Karin bayani: Girgizar kasa ta hallaka mutane 118 a China
Gidan talabijin na CCTV ya nuna gidaje masu tsayi da rufin gidaje da suka ruguje, yayin da ma'aikatan kashe gobara ke nufar wurin da girgizar kasar ta faru. Shi kuwa kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin ya bayyana cewa, hukumomin yankin na ziyartar gundumomi daban-daban na lardin Tibet domin tantance irin illar da girgizar kasar ta haifar. Ko da yake ana yawan samun girgizar kasa a yankin, amma iftila'in na wannan Talata ne mafi karfi da aka samu a tsawon kilomita 200 a cikin shekaru biyar na baya-bayan nan.