1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Girgizar kasa ta halaka mutane 32 a Philippines

Suleiman Babayo LMJ
June 8, 2026

Girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta hallaka fiye da mutane 30 a kasar Philippines.

Philippines I Girgizar kasa ta halaka mutane 32
Girgizar kasa ta halaka mutane 32 a PhilippinesHoto: GenSan DEV/Handout/REUTERS

Wata girgizar kasa mai karfin maki 7.8 a ma'aunin gwaji ta halaka kimanin mutane 32 a yankin kudancin kasar Philippines, inda wasu fiye da mutane 200 suka samu raunika, yayin da gidaje da dama suka ruguje.

Tuni ma'aikatan agajin gaggawa suka famtsama domin taimakon mutanen da wannan girgizar kasa ta shafa. Girgizar kasra ta Philippines ta janyo katsewar sadarwa da wutar lantarki cikin yankunan da aka samu bala'in.