Girgizar kasa ta halaka mutane a kasar Philippines
June 8, 2026
Hukumomi a Philippines sun tabbatar da mutuwar mutane takwas, tare da jikkatar wasu hudu a wannan Litinin, sanadiyyar afkuwar ibtila'in girgizar kasa mai karfin maki 7.8 a ma'aunin richter.
Karin bayani:ICC za ta kama tsohon shugaban 'yan sandan Philippines Rosa
Haka zalika girgizar kasar ta rusa gidaje da dama, tare da ingiza gargadin igiyar ruwan annobar tsunami a cikin kasar da kuma kasashen da ke yankin, wadanda suka hada da Indonesia da Palau da Taiwan da kuma Papua New Guinea.
Karin bayani: An tsige mataimakiyar shugaban Philippines Sara Duterte
A cewar babban jami'in 'dan sandan lardin Sarangani da lamarin ya faru, Major Roland Catoburan, gini ne ya danne mutanen da suka mutu a yankin Alabel, inda ya shawarci mazauna garin su koma yanki mai tsaundari na General Santos, domin kare kansu daga wannan masifa.
karin bayani: Kusan mutum 100 sun mutu sakamakon guguwa a Philippines
Tuni shugaba Ferdinand Marcos na Philippines ya sanar da rufe makarantu a tsibirin Mindanao da ibtila'in ya fi kamari, tare da ba da umarnin kwashe mutanen yankin.