SiyasaAsiya
Girgizar kasa ta halaka mutane kusan dubu a Afghanistan
September 1, 2025
Talla
Rahotannin daga birnin Kabul na cewa mutane sama da 800 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata sakamakon mummunar girgizar kasa a gabashin Afghanistan, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Taliban ta RTA ta rawaito.
Karin bayani: Afghanistan: Dusar kankara ta hallaka mutane 25
Ma'aikatar lafiya a Kabul da ke karkashin kulawar gwamnatin Taliban ta sanar da cewa har ya zuwa wannan lokaci suna ci gaba da tattara alkaluma tare kuma da zakulo mutanen da suka makale a baraguzai musamman a yankunan karkaka.
Karin bayani: Afghanistan: Gomman mutane sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa
Ko a shekara ta 2015, wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta halaka mutane sama da 350 a kasashen Afghanistan da Pakistan.