1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas a makomar gwamnatin Jamus

June 2, 2019

Shugabar jam'iyyar SPD a Jamus Andrea Nahles ta sanar a yau Lahadi cewa za ta sauka daga shugabancin jam'iyyar da kuma jagorancin rukunin yan jam'iyyar a majalisar dokoki bisa rashin goyon baya daga jam'iyarta

Andreas Nahles eine Neue -  SPD
Hoto: picture-alliance/dpa/U. Baumgarten

Nahles ta fuskanci matsin lamba sakamakon koma bayan da jam'iyyar ta samu da ke zama sakamako mafi muni a zaben majalisar dokokin Tarayyar Turai a makon da ya gabata.

Ta ce za ta ajiye mukamin shugabancin jam'iyyar ta SPD a gobe Litinin, yayin da a ranar Talata kuma za ta sauka daga shugabancin rukunin 'yan jam'iyyar a majalisar dokoki.

Murabus din na bazata ya sanya ayar tambaya akan makomar gwamnatin kawance ta Angela Merkel wadda dama take tangal-tangal. A yanzu dai Jam'iyar SPD ta Andrea Nahles, da kuma CDU ta Angela Merkel sune ke gudanar da gwamnatin kawance a Tarayyar Jamus, kuma idan har SPD ta janye daga kawancen, hakan na nufin gwamnatin Angela Merkel ta wargaje.