Turai sun cimma shirin ceton Girka
July 13, 2015Yarjejeniyar samar da shirin ceton wacce aka cimma bayan an kwashe sao'i 17 ana tattaunawa a daren ranar Lahadi tsakanin Girka da sauran kasashen kungiyar Tarrayar Turai da kuma Hukumar bada Lamuni ta Duniya IMF ta kunshi sauye-sauye da dama na tattalin arziki wanda zai sama wa Girka damar samun karin kudaden rance tsakanin biliyan 82 zuwa 86 a tsawon shekaru uku.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce hanyar za ta kasance doguwa kana kuma mai karangiya ga Girka dangane da wannan sabon shirin, ta ce kasarta za ta yi nazarin shawarar:
'Yan majalisar Jamus nada ta cewa
"Wannan shawara da kasashen kungiyar Tarayyar Turai guda 19 suka yanke zai bude hanya ga majalisar dokokin Bundestag ta Jamus ta kada kuri'a kan wannan shirin ceton tattalin arzikin na Girka"
Majalisun dokokin dai daban daban na kasashen Turai za su kada kuri'a a kan wannan batu watakila a cikin wannan mako ko ranar Talata ko ma Laraba ya dai danganta da tsarin da suka yi domin amincewa da shirin. Donald Tusk shi ne shugaban hukumar ta kungiyar Tarayyar Turai ya kuma yi karin haske:
"A yau manufofinmu daya ne bayan an shafe awowi 17 ana tattaunawa mun cimma gaci za a iya cewar mun cimma wata yarjejeniya".
Shirin tsuke bakin aljihun dai wanda masu bada bashi na Bankin Turai da sauran hukumomin kudi na duniya suka tilastawa Girka ya fi waccen tsanani wanda jama'ar kasar suka yi watsi da shi da kusan kashi 61 cikin dari, wanda kuma da alama yake zama saye ko fashi:
Kasuwannin shinku sun yi lale da matakin
Tuni dai kasuwanin shinku na Turai da na yankin Asiya suka yi lale marhabin da wannan yarjejeniya da aka cimma, kuma darajar takardar kudin Euro wacce a karshen mako ta fadi a gaban Dalar Amirka da kudin Yen na China, a yanzu ta sake rike matsayinta.
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce wannan masalaha da aka cimma za ta bada damar kare martabar kasashen na Turai da kuma darajar takardar kudin na Euro:
"Abin da muka ji tsoro shi ne cewar kasashen masu amfani da takardar kudin Euro su rabu da wata kasar wato Girka, wannan ayar tambaya an dade ana azata watanni kai shekaru ma".