Hukumomi a kasar Girka na ci gaba da daukar matakai da saka tsauraran dokoki, domin yaki da kwararar bakin haure daga Afirka da ke yunkurin isa kasashen Turai ta barauniyar hanya.
Sau tari dai bakin hauren na yin amfani da gabar ruwan Libiya, wajen shiga Turai Hoto: Hazem Ahmed/AP/picture alliance
Talla
Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis ne ya sanar da aniyar gwamnati na dakatar da yi wa bakin haure masu neman mafaka da suka fito daga Afirka daga gabar ruwan Libiya, a zauren majalisar dokokin kasar. Hukumomin Girka dai, sun ce matakin na wucin-gadi ne da zai shafe kimanin tsawon watanni uku yana gudana. Gwamnatin kasar ta ce a yanzu ta dauki matakin tsare 'yan Matakin na zuwa ne, a daidai lokacin da masu neman mafaka sama da 5,000 suka isa gabar Tsibirin Crete din a 'yan kwanakin nan. Sai dai Firaministan Mitsotakis ya danganta matakin kin yin rijistar bakin hauren, a matsayin somin tabi na daukar matakin ba sani ba sabo da gwamnatinsa za ta nuna kan lamarin shige da fice.
Libiya: Jahannama a tsakiyar Teku
03:46
This browser does not support the video element.
Kwararar masu neman mafakar ya haifar da cikas a fannin yawon bude ido a Tsibirin na Crete, kasancewar masu neman mafakar sun mamaye shi. Sama da bakin haure 2,000 ne suka biyo ta gabar Tekun Bahar Rum a karshen mako, abin da ya sa adadinsu ya kai dubu 10 a cewar alkalumman jami'an da ke gadin gabar ruwan. Firaministan Mitsotakis na Girka ya ce, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen taka wa bakin hauren birki. Firaministan Girkan ya sanar da zauren majalisar dokokin kasarsa cewa duk wasu bakin hauren da suka shiga kasar ta hanyar da ba ta dace ba, za a cafke su a kuma tsare su a wani mataki na mayar da martani ga masu safarar bakin hauren da kuma wakillansu.
Tunawa da bakin haure a Lampedusa
Lampedusa waje ne da bakin haure da ke son zuwa Turai kan je. Mahamadou Ba dan Senegal ne da ke zaune a Portugal, kamar sauran bakin haure shi ma ya taba zama a Lampedusa. Hotonsa na nuna halin da bakin haure ke ciki.
Hoto: Mamadou Ba
Kofar Lampedusa
Tsibirin Lampedusa da ke kasar Italiya waje ne da bakin hauren da ke son shiga Turai kan je. Mahamadou Ba dan kasar Senegal na zaune a Portugal tun shekara ta 1997 kuma ya sha zuwa Lampedusa. Mutumin dan rajin kare hakkin bil adama ne kuma hotonsa a nan na nuna irin halin da bakin haure suka shiga a tsibirin Lampedusa da tekun da ke kusa da shi.
Hoto: Mamadou Ba
Jiragen ruwa sun zama tamkar wata makabarta
Jiragen ruwan nan da makamantansu sun zame wa bakin haure tamkar wata makabarta. Galibin bakin haure kan isa Lampedusa ne da irin wadannan kananan jiragen ruwa inda su kan gamu da hadarin da ke yin ajalinsu. Hadari mafi muni ya auku ne ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2013 inda mutane 366 suka mutu yayin da sojin ruwan Italiya suka ceto mutane 200 a cikin watan Janairun da ya wuce.
Hoto: Mamadou Ba
Mutuwa kan hanyar neman rayuwa mai inganci
Ana daukar Lampedusa tamkar wata makabarta ga dubban bakin haure. "Mutane na mutuwa don neman rayuwa mai inganci" kamar yadda Mamadou Ba ya nunar. Kimanin mutane 400 ne suka rasu a watan Oktober shekarar 2013 lokacin da wasu jiragen ruwa biyu suka yi hatsari yayin da suke kan hanya daga arewacin Afirka zuwa Lampedusa. Galibin wanda suka rasu sun fito ne daga kasashen Eritrea da Somaliya.
Hoto: Mamadou Ba
Abubuwan da za a tuna bakin haure da su
Galibi ba a da cikakkun bayanai game da asalin bakin hauren da kan rasu a Lampedusa lokacin da suke kokarin shiga nahiyar Turai. Yawanci ababen da ake tunawa da mutanen su ne irin wadannan rigunan da sauran kayayyakin da ake samu a jikin jiragen ruwan da suka nutse da bakin hauren da ke cikinsu.
Hoto: Mamadou Ba
Gidan adana kayan bakin hauren da suka rasu
Akwai wani gida na adana kayan tarihi musamman na bakin hauren da suka rasu sakamakon nutsewar jiragen ruwansu. Kayan sun hada da fasfuna da hotuna da kuma wasiku. Mamadou Ba ya ce kayan na sawa a tuna da wadanda suka rasu. Har wa yau kayan kan sa a fahimci yadda bakin haure suke da irin mafarkin da suke da shi.
Hoto: Mamadou Ba
Abubuwan da bakin haure kan yi yau da kullum a kan teku
Bakin haure kan gudanar da irin dabi'un da suka saba kan teku lokacin da suke kokarin ketarowa zuwa nahiyar Turai. Galibi irin wannan yunkuri nasu na kasancewa mai hadarin gaske. Babu dai tabbas ko irin wadannan tukwanen da ke ajiye a gidan adana kayan tarihin bakin hauren na wadanda suka mutu ne ko kuma wanda suka rayu amma kuma kayansu suka salwanta.
Hoto: Mamadou Ba
Tunawa da rayukan wadanda suka rasu
Akwai wurare da dama da ke tuna wa mutum bakin hauren da ke zaune a tsibirin Lampedusa mai tsawon mil tara. "Wajen kan sa a tuna da wanda ke raye da kuma wadanda suka rasu'' kamar yadda Mamadou Ba ya nunar. Lampedusa dai na da nisan kilomita 205 kudu da tsibirin Sicily na Italiya kazalika yana makotaka da Tunisiya wadda tazararsu ba ta wuce kilomita 130 ba. Lampedusa wani tsani ne na shiga Turai.
Hoto: Mamadou Ba
Bukatar fidda sabbin manufofi kan bakin haure a Turai
Wannan wajen da ke zaman maboya lokacin yakin duniya na biyu wata alama ce ta hadewar kungiyar tarayyar Turai. A cikin watan Fabrairun da ya gabata wakilan kungiyoyin fararen hula 400 sun yi zanga-zanga inda suka fidda sanarwa kan bukatarsu ta neman sabbin manufofi kan bakin haure a Turai. Kungiyoyin sun bukaci karin mutunta 'yancin bakin haure duba da yadda da dama ke mutuwa a kan iyakokin Turai.
Hoto: Mamadou Ba
Lampedusa daura da kogin Bahar Rum
Mazauna wannan karamin tsibiri na Lampedusa da ke kogin Bahar Rum kusa da Sicily da arewacin Afrika na fatan samun ingantacciyar rayuwa. Da dama dai na ganin idan aka yi gyare-gyare kan manufofin kasashen Turai game da bakin haure, kwararar bakin da ake samu da kuma hadurran da suke gamuwa da su za su ragu matuka.
Hoto: Mamadou Ba
Hotuna 91 | 9
A baya-bayan nan dai wakilan Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ministocin kasashen Girka da Malta da Italiya, sun tattauna da gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniyar karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibeh a birnin Tripoli dangane da shawo kan matsalar kwararar bakin haure da ke kwarara zuwa kasashen Turan. Kungiyar Tarayyar Turai EU ta ce, za ta binciki matakin da hukumomin Athens suka dauka na dakatar da rijistar masu neman mafaka na wani dan lokaci daga Afirka yayin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi tir da matakin.