1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka gwamnatin hadaka a Jamus ya gamu da cikas

Yusuf Bala Nayaya
November 21, 2017

Batun 'yan gudun hijira na cikin abin da ya hanawa jam'iyun CDU/CSU da FDP da Greens cimma matsayar kafa gwamnatin hadaka.

Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A yayin da hankali ya soma karkata zuwa ga batun shirya sabon zabe bayan rushewar batun hadakar jam'iayun kafa sabuwar gwamnati, yanzu haka wasu shugabannin siyasar Jamus sun soma yin kiraye-kirayen nuna dattaku domin kaucewa jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Shugaba Merkel tare da wakilan wasu jam'iyyuHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a wannan rana ta Litinin cewa za ta yi kokari na ganin komai ya daidaita a kasar bayan da jam'iyyar masu kare manufofin kasuwanci ta Free Democratic Party ta balle daga shirin kawancen kafa gwamnati. A cewar Merkel dai jam'iyyun da suka shiga wannan kawance na CDU da CSU da Green da FDP tattaunawarsu ta yi nisa kafin tsakiyar daren jiya ana daf da kammalawa jam'iyyar ta FDP ta balle, Merkel ta ce duk da cewa ta mutunta matsayar jam'iyyar amma dai abin takaici ne inda ta ke cewar:

"Mun dauka muna kan tafiya ce wacce za mu kai ga karshenta, duk kuwa da cewa mun tsammaci dama za a fiskanci kalubale."

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela MerkelHoto: picture alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Wannan dai shi ne karon farko a cikin shekaru 70 na baya bayan nan a tarihin siyasar kasar da Jamus ke tsintar kanta a cikin wannan yanayi, na kasa kafa kawance mai rinjaye da zai girka gwamnati bayan gudanar da zabe. Kuma idan har shugabar gwamnatin Jamus ta kasa cimma wannan buri a nan gaba ba abinda zai rage mata illa sake shirya zaben 'yan majalisar dokokin na gama gari.Tattaunawar kafa gwamnati a Jamus

Manyan batutuwa da suka zamewa zaman taron kadangaren bakin tulu dai na zama batu na 'yan gudun hijira da sauyin yanayi. Merkel dai ta bayyana cewa za ta sanar da shugaban kasar ta Jamus Frank Walter Steinmeier a hukumance matsayar da suka cimma da sanin mataki na gaba da za a dauka. Jamus: Merkel ta tabbatar da shirin kafa kawance

Zaben Jamus: Merkel mai sauyin manufofi

01:08

This browser does not support the video element.