Girka na fuskantar barazanar sake zaɓe
May 12, 2012Shugaba Karolos Papoulias na Girka ya sake gayyato shugabannin jam'iyyun siyasar ƙasar, a wani yunƙuri na ƙarshe na hana sake gudanar da wani zabe. Hakan ya kasance ne, bayan da shugaban jam'iyyar gurguzu Evangelos Venizelos, ya zame shugaban jam'iyya ta uku daya sanar da gaza kafa gwamnatin haɗin gwiwa. 'Yan siyasan Girkan dai na fuskantar banbancin ra'ayi dangane da shirin tsuke bakin aljihu mako guda bayan kammala zaben kasar. Batu da a hannu guda ya bar wakilan majalisar dokokin suma da rarrabuwar kawuna, tsakanin masu goyon baya da kuma adawa da tsarin kuɗaden ceto na hadin gwiwar Kungiyar gamayyar Turai da hukumar bada lamuni ta IMF. Gazawar shugaba Karolos Papoulias wajen shawo kan jam'iyyun su kafa gwamnatin haɗaka, na nufin sake gudanar da zaɓe a watan Yuni. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai na nuni da cewar, mafi yawan al'ummar kasar na goyon bayan jam'iyyar dake adawa da tsarin ceton kasar daga matsalar karayar tattalin arziki, batu da ka iya illata wakilcin Girkan, a tsakanin gungun ƙasashe masu amfani da takardan kuɗi na Euro.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe