Girka na kan hanyar samun ƙarin tallafi
February 16, 2012Talla
Yarjejeniya dai ta tanadi rage kuɗaɗen da gwamnatin ta ke kashewa da biliyan dubu 325 a shekara ,gabannin samun zagaye na biyu na tallafin da suka yi mata alƙawari.Wannan sharaɗi wanda shi ne kusan na ƙarshe da hukumomin ba da lamuni suka buƙaci Girka ta amince da shi. Zai sa gwamnatin ta rage albashi ma'aikata tare da rage kuɗaɗen pansho da kuma salamar wasu maaikatan daga bakin aiki.
Nan gaba ne aka shirya ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarrayar Turai zasu sake yin wani zaman taro domin yanke hukumci akan taimakon na biliyan dubu 130 da za a bai wa Girkan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Awal