Girka sabuwar Majalisar Wakilai ta Libiya
August 8, 2012An shirya shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Mustafa Abdeljalil zai miƙa iko ga sugaban wuccin gadi yan majalisar mai wakilai 200 wacce za ta kula da rubuta sabon kudin tsari mulki na ƙasar da zai kai ga shirya wasu zaɓbuƙa bisa ta farki na dimokaradiyya.
Tun da farko jama'a sun yi ta yi mamaki dangane da sakamakon zaɓen yan majalisun wanda shi ne karo na farko da aka gudanar a cikin shekaru goma wanda ya kai ga bai wa ƙawancen jam'iyyun siysar masu sasaucin ra'ayi ta tsohon framinista Mahmud Jibril samun rinjaye a zaɓen
An dai yi tsamanin ga irin abinda ya faru na juyin juya hali a cikin wasu sauran ƙasashen larabawar, masu kishin adinnin islamar zasu yi galaba a zabe to amma sai abin ya sha banban.
Ana tsamani samun wani sabon ƙawance a cikin majalisar
Du dama yadda majalisar ta wakilai ta kasu a kaso daban daban na jam'iyyun siyasar da kuma yan takara indepanda ,babban abinda ake jira ga majalisar shi ne na rawar da zata taka ga ƙasar da ta yi fama da juyin juya halin da ya kawo ƙarshen mulkin kama karya na kanal Gaddafi na kusan shekaru 40 domin sake samun yardda jama'a tare da dawo da kwanciyar hankali da kuma doka a oda.Kurt Pelda wani ƙwarrare akan Libiya ya shaida wa DW cewar saɓanin da ke tsakanin yan siyasar ba zai hanna su ba yin hulɗa ba ''ya ce mai yiwa ne masu kishin islama su shawo kan yan indepanda domin taka wata muhimiyar rawa a majalisar don yin wani ƙawance.
A na tuanani cewar majalisar za ta yi kokarin magance irin mumunar abubuwan da aka yi fama da su a zamanin mulkin kama karya ; wanda a ƙarƙashin mulkin Gaddafi wanda ya fara mulki tun a shekara ta 1969 yankin Syrte inda nan ne maihafarsa da Tripoli suka fi cin moriyar arzikin man fetir da ƙasar ta ke da shi , kuma sauran yankuna sun yi ta fama da wahaloli, ''ya ce a zamani mulkin Gaddafi ababan da suka shafi hanyoyi da titina da sauran kayayakin gine gine an yi sakaci akan su, ya a ce a yanzu aikin fitar da ɗanya man fetir ɗin ya na tafiya da kyau, sai dai babu gyara na kayayakin da ake yi abinda ka iya zama babbar matsala a gaba inda ba a ɗauki mataki.
Brazanar ga taɓarɓarwar al'amuran tsaro
A yankunan da dama na ƙasar Libiya ɓangarorin al 'umma daban daban ko wane na da nasa mayaƙan sa kai dole ne sai gwanatin ta kirshe domin tabbatar da tsaro .Abinda ake ganin babban ƙalubale ne dake a gaban sabuwar majalisar shine na kawance ɗamarar mayaƙan kamar yadda wani dan jarida Laswad ya baiyana wa DW ''ya ce maganar tsaro a Libiya wani abu ne da ke da mahimanci a yanzu ya ce a kwai gomai na duban jama'a da ke ɗauke DA makamai waɗanda ba su cikin ƙaida ya ce ƙwance ɗamarar' waɗannan mayaƙa shi ne babban tushen tabbatar da tsaro.
Na gaba ne dai inda sun fara zaman taron sabbin yan majalisar na CGN zasu zaɓi shugaba da wasu mataimaka guda biyu ,a lokaci ne kuma za a rusa gwamnatin wucin gadin ta CNT: za dai a gudanar da taro majalisar ne a cikin tsatsauran matakan tsaro a daidai lokacin da rahotanni ke ambato cewar an kama wasu mutane guda ukku a cikin wannan mako a birnin Tripoli waɗande ƙoƙarini tayar da bama bamai.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi
Daga ƙasa za a iya sauran wannan rahoto