1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta kama wani jirgin ruwan Rasha

Abdourahamane Hassane
April 19, 2022

An kama wani jirgin ruwa na dakon man fetir na Rasha a kasar Girka a karkashin takunkumin da kasashen Turai suka kakaba wa kasar wanda ke da alaka da yakin Ukraine.

Vermisstes Schiff Arctic Sea
Hoto: AP

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ce jiragin ruwa na kasa da kasa da ke dauke da mutane 19,da ake kira da sunan Pegas wanda yakamata ya isa tashar jiragen ruwa ta Marmara a kasar Turkiyya a halin yanzu yana can a Karystos da ke kudancin tsibirin Euboea na kasar Girka.