1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta samu karin tallafi

February 21, 2012

Bayan kai ruwa rana daga karshe dai kasashen dake amfani da kudin Euro sun amince da baiwa kasar Girka tallafi na Euro biliyan 130

Evangelos Venizelos ministan kudin Girka ke tattaunawa da takwarorinsa a taron baiwa kasar tallafi
Eurogroup Treffen in BrüsselHoto: Reuters

Ministocin kudi na kasashen dake amfani da kudin euro sun cimma yarjejeniyar baiwa kasar Girka tallafi karo na biyu, domin tsamota daga rugujewar tattalin arziki. An cimma matsayar bayan tattaunawar sa'o'i 12 a birnin Brussel, wanda aka kammala safiyar yau Talata. tallafin da za a baiwa Girka ya kai euro biliya 130. Masu bin kasar bashi sun amince da yafe kashi 53 cikin dari na kudin da suke bin kasar. Jagoran kasashen dake amfani kudin euro kana Firayim ministan kasar Loxemburg Jean- Claude Junker ya shaidawa manama labarai cewa sun samu nasarar ceto makomar Girka cikin kasashe masu amfani da kudin euro. Yarjejeniyar ta tanadi cewa wata hukuma ta musamman daga kasashen masu amfani da euro tare da asusun bada lamuni na duniya, za su rika sa ido kan yadda Girka ke tafiyar da harkokin kudinta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal