Girka ta samu kudin ceto tattali arzikinta
February 21, 2012Bayan kai ruwa rana daga karshe da ministocin kashen dake amfani da kudin euro sun amince da baiwa kasar Girka tallafi karo na biyu, domin tsamo kasar daga cikin halin tattalin arzikin da ta fada. Wannan ceton dai ya zo wa Girka ne a dab da kaiwa ga kasar ta kasa yin komai ta fanni kudi.
Taron wanda ya dauki ministocin kudin sa'o'i 12, ya cimma yarjejeniyar da za ta yi tasiri bawai ga kasar Girka kadai ba harma ga makomar sauran kasashen dake amafani da takardar euro, wanda dama can rikicin kudun Girka ya yi wa lahani. A shirin da ministocin suka amince za a bawai Girka tallafin euro biliyan130, kana suma kamfanoni masu zaman kansu dake bin kasar ta Girka bashi sun yafe mata sama da kashi 53 cikin dari na bashin da suke binta, adadinda ya zarta yadda aka zata. Christian Lagarde shugabar asusun bada lamuni na duniya wato IMF ta yi karin haske...
"Mun fara zaman namu da ragewa kasar bashin cikin gida na sama da kashi 120, don haka mun samu nasara mai karfi a daran jiya, wanda za ta sa harkokin kasar Girka cikin matsayi mafi kyau, a yunkurinta na warware rikicin da take fama da shi tun makwanni"
Batun rugujewar tattalin arzikin kasar Girka dai ya jima yana kan kane al'umaran siyasa da na tattalin arzikin Turai, inda kusan ko wane taron da suka yi shi ke kasancewa a gaba. Olli Rehn shine ministan kudi na kungiyar Tarayyar Turai.
Yace "har ila a daran jiya ina samun labarin cewa kallo ya koma kasar Girka, amma daga karshe dai mun cimma matsaya"
To sai dai yayinda ake can a birnin Brussels ana hada takardu bayan cimma yarjejniya, ga al'ummar kasar Girka dake boren adawa da shirin wadanda kuma sune tsuke bakin aljihun gwamnati zai shafa, basa wani murna duk da wannan yarjejeniyar kamar yadda wannan malamin makaranta yake cewa.
"Duk daya ne koma nawane yawan kudin da aka bamu, idan dai tattalin arzikinmu bai inganta ba, idan dai ba su yafe daukacin basukan da suke binmu ba, idan dai babu adalci a lamarin, to kuwa ba za mu taba fita daga tashin hankalin da muke ciki. Wannan siyasar ta karyace, babban karya ma"
Itama wata matar aure da aka tambayi ra'ayinta bisa tallafin da ministocin kudi suka baiwa kasar, kada kai ta yi tana mai cewa.
"Banga wani haske a lamarin ba, wannan bai taimakawa basukanmu ba. Muddin dai kasarmu bata iya yin wani abu da kanta, bata iya saffara kayanta da kanta domin ta sake dogaro da kanta"
Karkashin wannan yarjejeniyar da aka cimma na baiwa kasar ta Giraka tallafi, an kafa mata tsauraran matakai, wadanda suka hada da dole ta riga fayyace duk wata harkar kudi, inda za kafa wata hukumar hadin gwiwa tsakanin kasashen masu amfani da kudin euro da kuma asusun bada lamauni, hukumar da za ta sa'ido kan yadda kasar ta Girka ke tafiyar da duk wata mu'amala ta kudi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasiru Awal