1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Gobara a asibiti da ke Indiya

Suleiman Babayo
December 17, 2018

Mutane shida sun halaka yayin da wasu fiye da 130 suka samu raunika sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibiti da ke Indiya.

Frankreich Paris Proteste Gelb-Westen Gilet Jaunes
Hoto: Getty Images/A. Jocard

Wata gobara da ta tashi a wani asibitin gwamnatin da ke birnin Mumbai na kasar Indiya ta halaka kimanin mutane shida, yayin da wasu fiye da 130 suka samu raunika. 'yan sanda sun ce godabarar ta tashi daga hawa na hudu na asibitin mai hawa biyar, inda 'yan kwana-kwana da masu aikin ceto suka taimaka wajen dakile wutar da ta tashi.

Ana yawan samun tashin gobara a kasar ta Indiya inda ake zargin sakaci kan rashin daukar matakan kariya da suka dace.