1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gobara a cibiyar man Guinea Conakry ta kashe mutane 11

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 18, 2023

Tuni dai aka sanar da rufe makarantu da ma sauran wuraren taruwar jama'a a babban birnin kasar, tare da rufe wasu hanyoyi, inda wasu ke hasashen cewa a iya fuksantar karancin man fetur a kasar a dalilin gobarar

Hoto: Zhang Jian/Xinhua/picture alliance

Hukumomi a kasar Guinea Conakry sun tabbatar da mutuwar mutane 11, tare da jikkatar wasu 88, sakamakon wata gobara a babbar cibiyar rarraba man fetur din kasar a Conakry babban birnin kasar.

Karin bayani:Shekaru biyun mulkin soja a Guinea Conakry

Shugaban hukumar kare hakkin ma'aikatan kasar ta Guinea Laftanar Kanar Jean Traore ya ce gobarar ta fara ne da tsakar daren Lahadin nan, kuma adadin mamatan ka iya karuwa, La'akari da irin munin raunin da wasu mutanen da ibtila'in ya shafa suka samu.

Karin bayani:Jagoran 'yan adawa zai yi takara a Guinea

Tuni dai aka sanar da rufe makarantu da ma sauran wuraren taruwar jama'a a babban birnin kasar, tare da rufe wasu hanyoyi, inda wasu ke hasashen cewa a iya fuksantar karancin man fetur a kasar a dalilin gobarar.