1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a Jamhuriyar Nijar

April 15, 2021

Gobara ta hallaka yara yan makaranta sama da ashirin a Jamhuriyar Nijar tuni kuma aka fara zaman makoki a kasar.

Symbolbild I Brandrodung für Palmöl-Plantagen
Hoto: Ulet Ifansasti/Getty Images

Akalla yara yan makaranata 20 suka rasa rayukkansu sakamakon wata gobara da ta tashi a wata makaratar boko mai dalibai sama da dari takwas a birnin Yamai fadar gwamnatin kasar. Shugaban hukumar kashe gobara na kasar Colonel Bako Boubacar ya ce kawo yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa gobarar ba da ta rutsa da yaran kanana da ke azuzuwan kasa da firamari. Baya ga yaran da suka rasa rayukkansu, gobarar ta kone azuzuwan daliban kurmus.