1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gobara ta halaka dalibai 17 a Kenya

September 6, 2024

Wata gobara da ta tashi a wata makaranata a Nairobi babban birnin kasar Kenya. Sai dai ba a iya tantance gawarwakin wasu dalibai ba kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar ta sanar.

Wani Jami'in kashe gobara na aikin ceto a Kenya
Wani Jami'in kashe gobara na aikin ceto a KenyaHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kenya Resila Onyango ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto musamman na ragowar daliban da suka makale a ginin makarantar ta Hillside Endarasha Academy da ke yankin Nyeri, inda ta ce baya ga dalibai 17 da suka mutu, akwai wasu guda 14 da suka samu munanan raunuka.

Karin bayani:Gobara ta halaka jama'a a Kenya 

Ana yawan samun gobara a makarantu da gine-gine da ke kasar ta Kenya. Ko a shekara ta 2017, wata mummunar gobara ta halaka dalibai 9 a wata makaranta da ke babban birnin kasar Nairobi.