SiyasaAfirka
Gobara ta halaka fursunoni 38 a Burundi
December 7, 2021Talla
Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Burundi ta ce matsalar lantarki ce ta haifar da gobarar a wannan Talata, lamarin da ya tayar da hankulan mutanen wannan karamar kasa da ke gabashin Afirka. Rahotanni sun ce sai da fursunonin suka yi sa'o'i biyu suna ci da wuta kafin ma'aikatan agaji su halarci wurin.
A watan Agustan da ya gabata ma dai an samu gobara a gidan yarin da lokacin ma hukumomi suka ce fashewar abubuwan lantarki ce ta haifar da ita. Gidan kason na Gitega shi ne na uku mafi girma a Burundu kuma ya zama fitaccen wuri da ake zaunar da fursunonin siyasa. Sai dai ya jima a cunkushe, inda kawo karshen watan da ya gabata fursunoni 1500 ke a cikinsa maimakon mutane 400 da aka tsara ajiyewa a gidan mazan.