Gobara ta halaka majinyata Corona a Masar
December 26, 2020Talla
Masu fama da cutar Corona akalla bakwai sun mutu a Masar sakamakon tashin gobara a asibitin da ake jinyan marasa lafiya a kusa da babban birnin Alkahira.
Hukumomin sun tabbatar da karin wasu mutane akalla biyar da gobarar ta jikkata, ba a gano musabbabin tashin gobarar a asibitin ba, amma jami'an kashe gobara sun shawo kan matsalar.
A watan Yuni, wasu majinyata sun mutu a wani asibitin shi ma inda gobara ta tashi yayin da wasu da dama suka jikkata.