1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijra sun rasa rayukansu a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
April 16, 2020

Masu aikin jin kai sun tabbatar da mutuwar 'yan gudun hijirar 11 a yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar wata gobara da ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar da ke Gamboru.

Nigeria | Brand auf dem Balogun-Markt
Wannan wani tsohon hoto ne da muka yi amfani da shiHoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Ya zuwa yanzu babu wasu bayyanan da suka tantance musabbabin gobara wacce ta lamushe daruruwan gidaje da kuma kayayyakin abinci da sutura na ‘yan gudun hijira da suka fito daga kananan hukumomi bakwai na Jihar Borno 7.Malam Bukar Muhammad wani ne da ya yi aikin jin kai a garin na Gamboru sakamakon tashin gobarar inda ya bayyana cewa yanzu hakan wuta na ci gaba da kamawa bayan ta kona wasu dakuna da dama. Haka kuma rahotanni daga wakilinmu na Jiahr Bauchi Aliyu Muhammad Waziri sun tabbatar da cewar wata gobarar ta tashi a babbar kasuwar jihar da ake kira Muda Lawal. Lamarin da ya haddasa tare da zama musabbabvi na mutuwar wani matashi daya, baya ga komnewar shaguna da dama.