Gobara ta hallaka mutane 59 a Macedonia
March 16, 2025
Mutane daga sassan duniya sun mika sakon jaje kan Iftila'in gobarar da ta faru a arewacin Macedonia
Galibin wadanda suka rasun matasa ne, sun sami kuna da shakewa da hayaki da kuma turmutsutsi a kokarin kaiwa kofa daya tilo na ginin a cewar jami'ai. Wasu yaran kanana ne da basu wuce shekaru 16 da haihuwa. ba.
Ministan cikin gida Panche Toshkovski ya ce an kama mutane 15 da ake tsare da su domin amsa tambayoyi bayan da binciken farko ya nuna gidan rawar ba shi da lasisi. Ya ce yawan mutanen da ke cikin gidan rawar a lokacin da iftala'in ya faru sun rubanya fiye da adadin mutane 250 da jami'ai suka yi kiyasin gidan zai dauka.
Shugabar hukumar tarayyar Turai da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky sun aike da sakon jaje tare da fatan samun sauki ga wadanda suka sami raunuka.