Gobara ta hallaka mutane 70 a Mozambik
November 18, 2016Talla
Fiye da mutane 70 sun hallaka sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da mota tankar mai ta kama da wuta a yankin tsakiyar kasar Mozambik. Kafofin yada labarai na kasar sun ce akwai kimanin mutane 100 da suka samu raunika, kuma akwai yara a ciki.
Mahukunta sun kaddamar da binciken sanin ko ana sayar da man ne lokacin da lamarin ya faru, ko kuma mazauna yankin ne suka yi wa motar kwantan bauna. Tuni gwamnatin kasar ta Mozambik ta tura ministoci uku zuwa wajen da aka samu gobatar domin gani da ido da sanin hakikanin abin da ya faru.