1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta kashe mutane masu yawa a Niger Delta

October 3, 2023

Cikin mutanen da gobarar ta kashe har da mace mai juna biyu wadanda dukkaninsu suka kone kurmus.

Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wata gobara da ta tashi a wata matatar man fetur ta bayan fage a yankin Neja-Delta a Najeriya ta hallaka mutane kimanin 37 da suka kone kurmus, cikin su har da wata mata mai dauke da juna-biyu, wasu da dama kuma suka jikkata, kamar yadda mazauna yankin da ma wata kungiya mai fafutukar kare matasan yankin wato Youths and Environmental Advocacy Centre suka tabbatar.

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce gobarar ta tashi ne jiya a kudancin jihar Rivers, inda ake tace man ta barauniyar hanya, amma ba ta yi wani cikakken bayani a kan lamarin ba.

Tashin gobara a irin wadannan wurare da ke da arzikin man fetur da ake hako shi tare da tace shi ta barauniyar hanya ba sabon abu ba ne.

Hukumomin Najeriyar dai sun ce daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa Fabarairun 2022, kasar ta yi asarar dala biliyan uku a dalilin aikin irin wadannan tsageru da ke kafa wuraren hakar man da kuma tace shi ba bisa ka'ida ba.