SiyasaAfirka
Gobara ta jikkata mutum 25 a Masar
October 2, 2023Talla
Rahotanni sun ce ba a sami hasarar rayuka ba kuma an sami shawo kan gobarar.
Bakin hayaki ya turnuke ginin a yayin da gobarar ta tashi.
Kawo yanzu dai ba a san musababbin tashin gobarar ba.
Ana dai yawan samun tashin gobara a Masar inda ake da karancin fadakarwa kan tashin gobara da kuma jinkiri wajen kai agajin gaggawa.
A watan Augustan 2022 gobara ta hallaka mutane 41 a wani coci a birnin Alkahira inda aka rika kiran samar da ingantattun kayan aiki ga ma'aikatan kwana kwana.