Fursunoni hudu sun mutu a Tehran
October 16, 2022![Gobara a gidan yarin Evin a Iran](https://static.dw.com/image/63454350_800.webp)
Talla
Hukumomin gidan yarin Evin ba su bayar da cikakkun bayanai kan dalilin tashin gobarar da kuma rikicin da ya barke tsakanin fursunonin ba.
Sai shedu sun ce a ranar Asabar an jiyo fashe-fashe da dama a cikin gidan yarin, bayan da gobarar ta tashi abin da jami'an kula da gidan yarin suka bayyana da rikici na cikin gida.
An shafe makonni ana zanga-zanga a Iran tun bayan sanar da mutuwar Masha Amini mai shekaru 22 a ranar 16 ga watan Satumba, kwanaki uku bayan da jami'an 'yan sanda suka kama ta a Tehran bisa zargin keta ka'idojin shigar mata a kasar.