1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Gobara ta kone masana'antar kera makaman Turkiyya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 24, 2024

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 12 a fashewar wasu abubuwa a masana'antar kera makamai da ke Arewa maso yammacin kasar.

Türkei | Waldbrände in Izmir
Hoto: Berkan Cetin/Anadolu/picture alliance´

Wasu hotunan da aka fara yadawa sun nuna gilasai da karafa da suka tarwatse a wajen masana'antar, inda a gefe guda aka tanadi motocin daukar marasa lafiya na gaggawa.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiyya Ali Yerlikaya, ya ce zuwa yanzu ba a iya tantance dalilin fashewar ba amma sun kaddamar da bicike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Karin bayani:Turkiyya ta cafke wanda ake zargi da kai hari Coci a Santanbul

Gidan talabijin din kasar mai suna CNN da ke da alaka CNN din Amurka, ya nuna kai tsaye yadda wuta ke ci tare da turnukewar hayaki bayan rugurgujewar wani kamfani a kauyen Kavakli da ke lardin Balikesirm

Tuni aka tura jami'an kashe gobara da na lafiya don bada agajin gaggawa ga wadanda ibtila'in ya shafa, kamar yadda ma'aikatar yada labaran kasar ta sanar.

Karin bayani:Nakiya ta kashe rayuka a Turkiyya

Kamfanin da ke arewacin Balikesir yana kera alburusai da bama-bamai da harsasai don kasuwannin cikin gida da na waje.

Turkiyya ta zama babbar mai fitar da makamai zuwa kasashen waje, musamman ma jiragen yaki marasa matuka, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kasance babban mai goyon bayan masana'antar.