Shugaban kasar Faransa ya janye jawabin da zai gabatar
April 15, 2019Talla
Hayakin gobarar dai ya mamaye sararin samaniyar birnin na Paris abinda da ya firgita al'ummar kasar da kuma 'yan yawon bude ido, a nasa bangaren kakakin majami'ar ya shaidawa manema labarai cewar gobarar ta lakume dukkanin turakun dake dauke da rufin majami'ar bayan jami'an hukumar kashe gobara sun danganta tashin gobarar da sabunta ginin da yake gudana a yanzu haka, tuni shugaban kasar Emmanuel Macron ya isa gurin cikin juyayi bayan ya jingine wani jawabi da yayi shirin gabatarwa a kafar yada labaran kasar.